Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ministankula da harkokin addini na Masar ya fadi jiya cewa, gasar kur’ani ta duniya da za a gudanar a kasar an bata suna gasar Sheikh Khalil Husri domin tunawa da shi da kuma girmama shi.
Ministanya ce ko shakka babu kowa a duniya ya san irin gagarumar gudunmawar da sheikh Khalil Husri ya bayar a dukkanin bangarori da suka shafi kur’ani mai tsarki.
A kan haka y ace gasar wadda za a gudanar a cikin makonni uku masu zuwa a cikin lardin Jiza za ta samu sunan shehin malamin wand aba za a taba mantawa da shi da gudunmawarsa ba.
An haifi Khalil Husri a n Satumban 1917 a kasar ta masar, kuma his ne mutum na farko da ya fara karatun kur’ani da aka nada a cikin kaset.