Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin din Russia Today ta bayar da rahoton cewa, bayan Syria, kasashen Ukraine, Afghanistan, Iraki da Yemen ne aka fi kashe mutane a hare-hare a cikin shekara ta 2017 zuwa 2018.
Haka na kuma sakamakon binciken ya nuna cewa ban da kasashen Afghanistan da Ukraine, a cikin shekara ta 2018 hare-haren ta'addancin sun kara rauwa idan aka kwatanta da 2018 a kasashen Syria da Iraki.
A matsayi na duniya kuma , sakamakon binciken ya nuna cewa, a cikin shekara ta 2017 an kashe mutane dubu 27 a duniya, amma a cikin shekara ta 2018 an kashe mutane dubu 13 nea duniya a hare-haren ta'addanci.