IQNA

Cibiyar Azhar Bukaci Sanya Ido Kan Kafofin Sadarwa Na Yanar Gizo

23:10 - March 29, 2019
Lambar Labari: 3483504
Babbar cibiyar musulunci ta Azahar da ke kasar Masar ta bukaci gwamnatocin kasashen musulmi da su sanya ido kan kafofin sadarwa na yanar gizo domin yaki da ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Religion News ya bayar da rahoton cewa,a  cikin wani bayani da ta fitar jiya, cibiyar Azahar ta bayyana cewa, kafofin sadarwa na yanar gizo su ne manyan hanyoyin da kugiyoyin 'yan ta'adda musamman daesh, suka yi amfani da su wajen yada akidunsu.

Tarik Sha'aban Muhammad, daya ne daga cikin jami'an cibiyar Azhar, wanda ya bayyana cewa; a cikin lokutan nan cibiyar Azahar ta himamtu matuka wajen sanya ido a kan abubuwan da ake sakawa a cikin shafukan yanar gizo, wadanda suke da alaka da addinin muslunci, domin ta wadanann hanyoyin ne ake gurbata tunanin matasa suke shiga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Ya ci gaba da cewa,a  cikin 'yan shekarun da ba su hudu ba, kungiyar daesh ta kirkiri shafuka na twitter da suka kimanin dubu 46, wadanta ta yi amafani da su wajen yada akidunta na kafirta musulmi da kuma tunzura matasa wajen shiga ayyukan ta'addanci ad suann jihadi.

Jami'in na cibiyar Azahar ya ce, daya daga cikin manyan hanyoyin yaki da ta'addanci a halin yanzu ita ce sanya ido kan kafofin sadarwa, tare da yada mahanga mai kyau kan addinin muslucni, da kuma jawo matasa da ake yadara ta wadannan hanyoyi domin dora kan sahihiyar turba ta akidar musulunci.

3800238

 

captcha