IQNA

Yadda Ayoyin Kur’ani Suka Yi Tasir A zuciyar Dan Wasan Boxing Na Amurka

23:49 - April 05, 2019
Lambar Labari: 3483519
Bangaren kasa da kasa, Amru Saad wani dan wasan finafinai ne a kasar Masar ya bayyana cewa ayoyin kur’ani sun yi tasiria  ciki zuciyar Mike Tyson.

Kamfanin dilancin labaran iqna, Amru Saad ya bayyana cewa, a lokacin da ya bayar da wani fim dinsa kyauta ga Mike Tyson wanda ya kunshi wasu ayoyin kur’ani tsarki, a lokacin Tyson ya ji abin da ayoyin suka kunsa a nan take ya zubar da hawaye.

Wannan dan wasa na kasar Masar ya ce Mike Tyson mutumin kirki ne, domin kuwa na kasance tare da shi a lokacin da ya ziyarci Masar, mun je wasu wurare tare shi, saboda haka na ga halayensa.

An haifi Tyson ne a shekara ta 1966 a yankin Broklyn na birnin New a kasar Amurka, kuma ya tashia  yankin, inda a shekara ta 1992 aka daure shi tsawon shekaru biyu a gidan kaso, bayan fitowarsa kuma ya tasirantu matuka da addinin mulsunci.

Kafin nan yay i tafiya zuwa Saudiyya inda ya y aikin Umrah, ya kuma ziyarci wasu wurare masu tsarki da suke a cikin kasar.

Dangane da tafiyarsa zuwa Umra Mike Tyson ya bayyana cewa hakika ya yi farin ciki maras misiltuwa, tun ya ziyarci wurare masu tsarki na addinin muslunci.

3800912

 

 

 

 

captcha