IQNA

23:36 - April 18, 2019
Lambar Labari: 3483557
Kungiyar Ansarullah (alhuthi) mai gwagwarmaya da mamayar saudiyya a kasar Yemen, ta bayyana matakin da shugaban Aurka Donald Trump ya dauka na kin amincewa a dakatar da yaki a kan kasar Yemen da cewa, ya tabbatarwa duniya da cewa Amurka ce take yin yin yakin.

Kakakin kungiyar ta Ansarullah Muhammad Abdulsalam ne ya sanar da hakan, inda ya ce abin takaici ne yadda shugaban kasar Amurka da kansa ne ya fito kai tsaye ya yi fatali da kudirin da majalisar dokokin Amurka ta amince das hi, wanda yake kira da a kawo karshen duk wani mara baya ga Saudiyya kan yakin da take kaddamarwa kan al’ummar ksar Yemen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula da a ba su ji ba su gani ba  a kasar ta Yemen.

Abdulsalam ya ce; wannan mataki na Trump yana kara tabbatarwa duniya da cewa, Amurka ba wai kawai tana taya Saudiyya yaki a kan al’ummar kasar Yemen ba ne, a’a ita ce mai jagorantar yakin, sauran kuma duk karnukan farauta ne.

Domin kuwa a cewarsa ta in da Trump ya ga dama a yau da Saudiyya ta dakatar da kai hare-hare kan al’ummar Yemen, domin kuwa ba isa ta saba wa umarninsa ba, amma da yake batu ne da Amurka samun ribar cinikin makamai na dubban biliyoyin daloli daga gwamnatin ta Saudiyya cikin sauki, ba a bu ne da Trump zai maraba da duk wani batun dakatatr da shi ba, kamar yadda ya sha nanata hakan da bakinsa.

A ranar Talata da ta gabata ce majalisar dokokin Amurka ta amince da daftarin kudirin da aka gabatar, da ke yin kira da Amurka ta dakatar da duk wani taimakon da take bayarwa a yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al’ummar kasar Yemen.

3804715

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kudirin ، taimakon ، saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: