IQNA

23:40 - April 18, 2019
Lambar Labari: 3483558
Bnagaren kasa da kasa, mai baiwa Trump shawara kuma surukinsa ya c za a aiwatar da yarjejeniyar karni bayan azumi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran spunik ya habarta cewa, Jared Kushner mai baiwa Trump shawara kuma surukinsa ya c za a aiwatar da yarjejeniyar karni bayan watan Ramadan.

Trump ne ya kirkiro abin da ake kira da yarjejeniyar karni tare da hadin baki da wasu daga cikin larabawa musamman Saudiyya da Jordan da kuma Masa, da sunan warwae rikicin Isra’ila da Falastinawa.

Amma babbar manufar Amurka ita ce tabbatar da cewa an kawo karshen maganar dawowar Falastinawa da da Isra’ila ta kora da suke zaunea  wasu kasashe, da kuma shelanta alaka a bayyane tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila, da kuma kawo karshen batun kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta.

3804729

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: