IQNA

21:28 - April 23, 2019
Lambar Labari: 3483573
A Sri Lanka, adadin mutanen da suka mutu a jerin hare haren da aka kai a kasar ya haura dari uku kamar yadda ‘yan sanda na kasar suka sanar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, bayan kame mutane kimanin 40 da ake zarginsu da hannua  hare-haren Sri lanka, adadin wadanda suka mutu ya karu akamakon cikawar wasu da suka samu raunuka a hare haren na ranar Lahadi data gabata.

A halin da ake ciki ‘yan sanda a kasar sun cafke mutane arba’in da ake zargi da hannu a jerin hare haren da aka kai kan majami’u da kuma otel otel a a yayin bukukuwan Eister.

Gwamnatin kasar dai na mai zargin wata kungiyar islama ta cikin gida mai suna The National Thowheeth Jama'ath, da kai hare haren.

Tunda farko dai an bayyana adadin mutanen da suka mutu a 300, a daidai lokacin da wadanda suka raunana ya kai 500.

3805827

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، haura ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: