IQNA

23:49 - May 02, 2019
Lambar Labari: 3483597
Bangaren kasa da kasa, babban sakatare kungiyar Hizbullah a Lebanon ya bayyana cewa farfagandar yaki kan Lebanon da cewa yaki ne na kwakwalwa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, babban magatakardar Kungiyar Hizbullah ta Lebanon, Sayyid Hassan Nasarallah wanda ya gabatar da jawabi dazu a birnin Beirut ya ce; Idan HKI ta shiga da sojojinta kudancin Lebanon, za a tarwatsa su.

Sayyid Nasarallah wanda yake jawabi danagane da zagayowar lokacin shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar ta Hibzullah, Sayyid Mustafa Badruddin ya bayyana cewa; Shahidin yana cikin na farko-farkon wadanda su ka ba da gudunmawa a kafuwar Hizbullah, kuma ya kasance mutum ne ma’abocin addini, wanda yake kishin al’ummarsa da kuma kasarsa.

Da yake Magana akan masu tsorata Lebanon akan yiyuwar HKI za ta shelanta yaki akan Lebanon, Sayydi Nasarallah ya ce; Kurari ne kawai da kuma yakin kwakwalwa, kuma manufarsa a wannan lokacin ita ce tilastawa Lebanon ja da baya akan hakkokinsa.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa; Gwagwarmayar musulunci tana da karfin da za ta iya shiga cikin yankin Jalil dake karkashin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Shugaban na kungiyar Hizbullah ya kuma yi ishara da yadda sojojin Sahayoniya su ka kasa shiga Gaza, duk da cewa yanki ne wanda yake a killace na shekaru, don haka ba zai iya shiga cikin kudancin Lebanon ba.

3808300

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: