Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na myjoyonline ya bayar da rahoton cewa, sheikh Harun Agikum malamin addinin muslucni a kasar Ghana, ya tarjama kur’ani mai tsarkia cikin harshen Ashanti, wanda ya dauke shi tsawon shekaru 40.
Sheikh Abdulmumin babban limamin yankin ya bayyana wannan aiki da cewa yana da matukar muhimamnci ga dukkanin musulmin kasar.
Umar Sanda Ahmad babban limamamin sojojin kasar Ghana ya bayyana gamsuwarsa da yadda wannan aiki ya gudana a cikin nasara.
Ashanti daya ne daga cikin yarukan kasar Ghana,wanda ake magana da shia wani bangaren kudancin kasar da kuma kasar Ivory Coast, inda kimanin muaten miliyan 2.8 ne suka magana da wannan harshe a kasar Ghana.