IQNA

22:58 - May 05, 2019
Lambar Labari: 3483610
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin kasashe sun bayyana gobea  matsayin ranar daya ga watan Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Khalij Times ya habarta cewa, a kasar Australia musulmi za su dauki azumi gobe a  matsayin daya ga Ramadan.

Wasu daga cikin kasashe sun bayyana gobe a  matsayin ranar daya ga watan Ramadan mai alfarma.

A cikin bayaninsa ya bayyana cewa, a gobe idan Allah ya kai mu akwai taron buda baki wanda zai hada musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, da nufin kara karfafa dankon alaka tsakanin al'ummar musulmi da saran mabiya addinai.

Kasashe irin su Saudiyya ma za su dauki azumi a gobe, kamar yadda hadaddiyar daular larabawa ma za ta dauka.

Haka nan ma kasashen Turkiya Qatar da Kuwait da Lebanon da wasu yankuna na Iraki za su dauki azumia  gobe, yayin da kasashe irin su Palastine, Jordan, Masar, Sudan, Morocco, Aljeriya, Tunisia, Mauritaniya, ba za su tashi da azumi ba.

3808930

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: