IQNA

23:58 - May 29, 2019
Lambar Labari: 3483684
Bangaren kasa da kasa, an bude gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Nuwakshut na kasar Mauritania.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa,a  jiya Talata n aka bude babbar gasar kur'ani ta kasar Mauritaniya, tare da halartar kasashe da suka hada da Morocco, Tunisia, Aljeriya, Seegal, Najeriya, Mali, Turkiya, Masar da kuma mai masaukin baki Mauritania.

Ahmad Wuld Ahlu Dawud ministan ma'aikatr kula d harkokin addini na kasar ya bayyana cewa, wanna gasa kamar sauran wadanda ake gudanarwa a kowace shekara, kuma manufar hakan ita ce kara bunkasa lamarin kur'ani mai tsarki.

An kasa gasar zuwa bangarorin harda, tilawa da kuma tajwidi, kamar yadda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazoa  gasar.

 

 

3815469

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: