IQNA

23:56 - May 31, 2019
Lambar Labari: 3483691
Jami’an tsaron Isra’ila sun hana dubban musulmi gudanar da sallar Juma’a a yau a cikin masallacin Quds mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, tun a jiya ne aka baza jami’an tsaron yahudawa a kan dukkanin manyan titunan birnin Quds, musamman masu isa zuwa masallacin Aqsa mai alfarma.

Rahotoon ya ce da jijjifin safiyar yau an kara yawan jami’an tsaron yahudawa a ciki da wajen birnin Quds, inda suke daukar kwararan matakai a kan masu tafiya zuwa masallacin Aqsa domin sallar Juma’a.

Wannan mataki dai na zuwa ne da nufin hana gudanar da duk wani motsi da ked a alaka da ranar Quds ta duniya, inda bisa al’ada dubban daruruwan musulmi ne daga sassa daban-daban na Palestine suke halartar masalalcin Aqsa a wanann rana, inda bayan kammala sarra Juma’a, akan rera take da ke jaddada aniyar muuslmi da Falastinawa, kan cewa babu ja da baya dangane da batun Quds.

Ko a yau jami’an tsaron yahudawan sun kashe wani bafalastine dan shekaru 19  da haihuwa, bisa zargin cewa yana yunkurin kai musu farmaki da wuka.

 

3815940

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، palestine ، asabar ، ranar qods
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: