IQNA

A Tunisia An Hana Yin Kamfen Siyasa Da Sunan Addini

23:47 - June 10, 2019
Lambar Labari: 3483725
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Tunisia ta kafa dokar hana in amfani da snan addini wajen yin kamfe na syasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labaran Rasid ya bayar da rahoton cewa, a Tunisia an kafa dokar hana in amfani da snan addini wajen yin kamfe na syasa, ta hanyar yin amfani da sunan domin samun kuri'a.

Gwamnatin kasar Tunisia ta dauki wannan mataki ne a daidai lokacin da ake shirin fama kamfe domin fuskantar zabuka masu a kasar, inda ta ce a lokutan baya wasu sun yi amfani da irin wannan damar wajen yin kamfen siyasa, amma ta hanyar fakewa da addini domin jan hankulan jama'a.

Bayanin ya kara da cewa, za a dauki dukkanin matakan ad suka dace na shari'a  akan duk wanda aka samu da aikata hakan a lokacin kamfen siyasa.

Tun bayan kifar da tsohuwar gwamnatin Tunsia, masu kishin addini suka shiga cikin harkokin siyasa gadan-gadan a kasar, inda a halin yanzu suke da wakilci a cikin majalisa.

3818391

 

captcha