IQNA

23:55 - June 11, 2019
Lambar Labari: 3483728
Kwamitin kare hakkokin musulmi na kasar Birtaniya Islamic Human Rights Council ya bukaci da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi a Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na kwamitin IHRC ya bayar da bayanin cewa, a jiya kwamitin ya fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ya bukaci mahukunta a Najeriya da su saki Sheikh Ibrahim Zakzaky domin nema masa magani a wajen kasar, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

A cikin bayanin kwamitin na IHRC, ya bukaci sauran kungyoyin kare hakkokin bil adama na kasa da kasa da su sanya baki a cikin batun, domin neman gwamnatin Najeriya ta amince da hakan.

A kwanakin baya ne wata tawagar kwamitin ta ziyarci sheikh Zakzaky a Najeriya, bayan samun izini daga gwamnatin kasar domin su duba yanayin da yake ciki.

Bayanin kwamitin ya ce akwai bukatar a fita da malamin zuwa waje domin duba lafiyarsa a asibitocin kasashen ketare da suke da wadatattun kayan aiki, musamman ganin yadda yake fama da matsaloli, da suka hada hawan jinni, haka nan kuma guda ya daina aiki baki daya, yayin da dayen kuma yake fuskantar matsala.

3818544

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: