IQNA

Dakarun Yemen Sun Kai Harin Ramuwar Gayya Kan Saudiyya

22:54 - June 12, 2019
Lambar Labari: 3483731
Bangaren kasa da kasa, dakarun Yemen sun sanar da harba wani makami mai linzami kan filin jirgin saman Abha dake lardin Asir a kudu maso yammacin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin almasirah net ya bayyana cewa, mahukuntan Saudiyya sun ce harin ya jikkata mutum ashirin da shida sannan kuma an dakatar da zurga zurgar jiragen sama a yankin.

Kakakin rundinar sojin Yemen, Birgediya-Janar Yahya Sari, ya danganta harin makami mai linzami kan filin jirgin saman na ‘’Abha’’ da maida martini ga hare haren wuce gona da iri da kawancen da Saudiyya ke ci gaba da jagoranta kan Yemen din, da kuma ci gaba da killacewar da Saudiyyar ta shafe shekaru biyar tana wa filayen jiragen saman Yemen din, ciki har dababban filin jirgin saman Sanaa.

Lardin ‘’Abha’’ yana da matukar mahimmanci kasancewarsa wanda yake bada damar kai wa ga yankin Taif da kuma wasu sassa dake tsakiyar Saudiyya.

Kafin hakan dama kakakin kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen din ya ce zasu ci gaba da kai hare hare kan filayen jiragen sama da wasu wurare masu mahimmanci na Saudiyya da hadaddiyar daular Larabawa idan basu kawo karshen killacewar da suke wa filin jirgin saman birnin Sanaa ba, dama kasar ta Yemen.

Gidan talabijin din Saudiyya ya dora alhakin harin da ya ce na ta’addanci ne kan fararen hula ga Iran da kuma ‘yan Ansarullah din na kasar ta Yemen.

jamhuriyar musulunci dai ta jima tana musanta hannunta a hare haren daukan fansa da ‘yan Houtsis din suke kai wa Saudiyya, ko kuma taimaka masu da makamai.

Yau kusan shekaru hudu kenan da Saudiyya ta killace kasar ta Yemen, tare da hana zurga zurga ta jiragen sama dana ruwa a wannan kasa ta Yemen, lamarin da ya jefa kasar cikin bala’I mafi muni a duniya.

3818730

 

 

captcha