IQNA

23:41 - June 18, 2019
Lambar Labari: 3483750
Bangaren kasa da kasa, kungiyar malamai ta kasa da kasa ta dora alhakin mutuwar Mursi a kan Al-sisi da Saudiyya da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kungiyar malamai ta kasa da kasa ta sanar da cewa hukumomin Masar ne suka kashe tsohon shugaban kasar Muhamad Mursi da kuma kasashen larabawan da suke mara musu baya.

Ita ma a nata bangare kungiyar 'yan uwa musulmi cikin wani bayyani da ta fitar a wannan talata na cewa Hukumomin kasar Masar ne ke da alhakin kisan tsohon shugaban kasar Muhamad Mursi, idan aka la'akari da yadda aka tsohon shugaban kasar ya mutu, za a fahimci cewa gwamnati ta bi mataki mataki ne wajen aiwatar da kisan tsohon shugaban kasar Muhamad Mursi.

Sanarwar ta ce da farko an kebe tsohon shugaban ne wuri guda a gidan yari sanan an hana shi magani duk kuwa da cewa yana fama da rashin lafiya, an hana likitoci su diba lafiyarsa, sannan kuma an hana shi ganawa da lauyoyinsa har ma da iyalansa.

Har ila yau sanarwar ta ce Marigayi Mursi karamin hakin da ya kamata ya samu a gidan yari, bai samu ba, wanda hakan ke tabbatar da cewa shiri ne da gwamnatin ta yi tun a baya na kawar da marigayi tsohon shugaban kasar Muhamad Mursi.

Kafin hakan dai Kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta bukaci a gudanar da bincike kan mutuwar ta tsohon shugaban kasar ta Masar Muhamad Mursi.

3820368

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، malamai ، Masar ، Mursi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: