IQNA

23:53 - July 12, 2019
Lambar Labari: 3483833
Bangaren kasa da kasa, rahoton majalisar dinkin duniya ya yi nuni da irin mawiyacin halin da dubban kanan yara suke ciki yan kabilar Rohingya a Bangaladesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya kan sha’anin rikicin Myanmar ta gabatar da rahoto ga majalisar dinkin duniya a jiya, dangane da halin da dubban daruruwan ‘yan gudun hijira ‘yan kabilar Rohingya suke a kasar Bangaladash.

Rahoton ya ce ‘yan gudun hijirar suna cikin mawuyacin hali, kuma suna da bukatar taimako na gaggawa a irin wannan yanayi da suke ciki, musamman mata da kananan yara wadanda su ne suka fi saurin galabaita.

Jami’ar ta ce ta zagaya yankuna daban-daban a inda aka tsugunnar da dubban daruruwar ‘yan kabilar ta Rohingya  acikin bangaladash, kuma dukkanin wurare halin da suke ciki ba mai kyau ba ne, a kan haka ta bukaci da a sake yin dubi kan wannan batu, da kuma dayukar matakan da suka dace domin taimaka wadannan ‘yan gudun hijira.

 

3826067

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: