IQNA

15:57 - August 10, 2019
Lambar Labari: 3483932
Jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei (DZ) ya aike da sakonsa ga mahajjatan bana. 5/8/2019

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai tsira da amincin Allah su tabbata ga manzonsa amintacce, Muhammad cikamakin annabawa, da alayensa tsarkaka musamman hujjar Allah a bayan kasa, da sahabbansa da wadanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar kiyama.

Taron aikin hajji wanda ake gudanawa a kowace shekara, wata rahama ce ta ubangiji ga al’ummar musulmi. Kira ne a cikin kur’ani (ka yi kira a cikin mutane zuwa ga hajji) kira ne zuwa ga kowa wanda ya wanzu tsawon tarihi domin isa ga wannan rahama ta ubangiji, domin zukata da rayuka masu kaunar ubangiji su samu rabo daga wannan babbar albarka. A kowace shekara akwai darussa da ake samu daga aikin hajji, ta hanyar wasu daga cikin mutane ne kuma wadannan darussa da sakonni suke isa ga sauran al’ummar musulmi na duniya.

Acikin aikin hajji akwai ambaton Allah da ibada, wanda shi ne gishiki na asali wajen tarbiyya da daukakar mutum da kuma al’umma. Taro da haduwa a wuri guda alama ce da ke nuni da kasantuwar musulmi al’umma ce guda, haka nan kuma dukkanin motsi da kai-komo a cikin aikin hajji alama ce ta tauhidi. Dukkanin mahajjata suna yin komai tare, iri daya babu banbanci tsakanin mutane, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke yin nuni a takaice da hakikanin al’ummar musulmi. Kowane Ihrami da dawafi da sa’ayi da tsayuwa da jifa da motsi da zama a cikin aikin hajji, isahara ce zuwa ga wata taswira ta hakikanin musulunci.

 Musayar ilmomi da abubuwan mallaka tsakanin mutanen kasashe da yankuna masu nisa da juna, bayyana mahanga da masaniya da kuma samun labaran juna, da kawar da rashin fahimta, da kusanto da zukata, da samun fadaka kan makiya na bai daya, wannan babban sakamako ne na taron aikin hajji, wanda ba za a iya samun sa ta hanyar gudanar da daruruwan taruka a duniya ba.

Nuna barranta, wato nuna kin amincewa da duk wani nau’in rashin tausayi da zalunci da munanan ayyuka na barna na azzaluman shugabanni na kowane zamani, da kuma yin turjiya a gaban zaluncin masu girman kai, hakan na daya daga cikin manyan lamurra masu albarka na aikin hajji, kuma hakan dama ce ga al’ummomin musulmi da ake zaunta.

A yau barranta daga tungar shirka da kafircin masu girman kai wanda Amurka ce a gaba, hakan na nufin barranta ne daga kisan wadanda ake zalunta da siyasar neman yaki a duniya, yin tir da kungiyoyin ta’addanci irin su Daesh da Balack Water ta kasar Amurka, nuna rashin amincewar al’ummar musulmi da haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya masu kisan kananan yara da masu mara musu baya da kuma masu  ba su taimako, yin tir da siyasar Amurka da kawayenta da ke haddasa yake-yake a cikin yankin yammacin Asia da arewacin Afrika wanda ya jefa al’ummomi cikin matsananciyar wahala da musibu masu muni, yin tir da nuna wariya bisa bangaranci na yanki ko launin fata, yin tir da duk wasu munanan halaye na manyan masu girman kai da shishshigi da haifar da fitina wadanda suke kira zuwa gare su, sabanin kyawawan halaye madaukaka da kuma adalci da musulunci yake yin kira zuwa gare su.

Wadannan kadan ne daga cikin tarin albarkar hajji irin na annabi Ibrahim wanda musulunci ya kiraye zuwa gare shi, wannan wani babban bangare ne mai muhimmanci daga cikin manyan gishikai da al’ummar musulmi ta kafu a kansu, a kowace shekara wasu daga cikin musulmi suna tafiya aikin hajji, wannan aiki da yake a matsayin wani taro mai girma da yake cike da ma’anoni, wanda yake yin ishara da kuma kira gare mu baki daya da mu zama irin wannan jama’a da taru a wuri guda domin wannan aiki mai girma.

Masana na duniyar musulmi wadanda wasu daga cikinsu daga kasashe daban-daban suna halartar aikin hajji a halin yanzu, suna da babban nauyi da ya rataya a kansu. Wadannan darussa na hajji dole ne a isar da su zuwa ga sauran al’ummomi ta hanyar himma da kokarin masana, a isar musu da sakonni da ilimi da mahanga da zaburarwa da kuma gogewa da fadakarwa irin ta al’ummar musulmi da ke tattare da wannan aiki.

A yau daya daga cikin batutuwa mafi muhimmanci ga al’ummar musulmi shi ne batun Falastinu, wanda yake a kan gaba a dukkanin batutuwa na siyasar duniyar musulmi, a dukkanin mazhabobinsu da kabilunsu da harsunansu. Zalunci mafi girma a cikin karnonin baya-bayan nan ya auku ne a Falastinu. A wannan abin da ya faru, dukkanin abin da al’umma guda take da shi, da ya hada da kasarta, gidajenta, gonakinta, arzikinta da kaddarori, alfarmarta, asalinta, duka an kwace.

Wannan al’umma tare da taimakon ubangiji ba ta karaya ba, ba ta mika wuya ba, a yau tafi yadda take a jiya, ta fuskar turjiya da jarunta a fagen daga, amma kaiwa ga sakamakon da take bukata, yana bukatar taimakon dukkanin musulmi.

Makircin da ake kira yarjejeniyar karni, Amurka azzaluma da kawayenta masu cin amana suna shirin aiwatar da shi, wannan babban laifi ne a kan dukkanin’yan adam, ba al’ummar Falastinu kawai ba.

Muna kiran kowa wajen fitowa gaba-gaba domin rusa wannan makirci na makiya, da karfin Allah da ikonsa mun san cewa wannan makirci da ma wasu makirce-makircen na masu girman kai, za su rushe a gaban himma da imanin tungar gwagwarmaya.

Allah mabuwayi yana cewa: (( Shin suna nufin wani kaidi ne? to, wadanda suka kafirta su ne wadanda ake yi wa kaidi.)) Allah mai girma da daukaka ya yi gaskiya.

Ina rokon Allah da ya yi wa dukkanin alhazai gamo da katar da jinkai da lafiya, ya karbi ayyukansu na ibada.

 

Sayyid Ali Kahmenei

 

3  Zulhijjah 1440      -       5/8/2019

 

http://iqna.ir/fa/news/3833773

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: