IQNA

23:48 - August 14, 2019
Lambar Labari: 3483946
Bangaren siyasa, a lokacin da jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yake ganawa da tawagar kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, ya jaddada wajabcin ci gaba da yin turjiya a gaban mamaye Saudiyya da UAE a kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya karbi bakuncin tawagar kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen, ya ce; Saudiyya da Hadddiyar Daular Larabawawadanda su ka tafka manyan laifukan yaki a kasar Yemen, ba za su cimma abin da su ka yi nufi ba, domin suna kokarin karkatsa Yemen ne zuwa kananan kasashe, don haka ya zama wajibi a yi tsayin daka wajen kalubalantarsu.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya jinjinawa al’ummar Yemen, saboda tsayin daka da jajurcewar da su ka yi wajen fuskantar masu wuce gona da iri, sannan ya kara da cewa; Duk wata al’umma wacce ta yi imani da Allah madaukakin sarki da alkawalinsa za ta sami nasara, don haka al’ummar Yemen da ake zalunta za ta kai ga wannan nasarar.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma mika ta’aziyyarsa ta shahadar Sayyid Ibrahim Badruddin al-Huthy dan’uwan jagoran Ansarallah Abdulmalik al-Huthy, sannan kuma ya yabawa iyalan Badurddin saboda tsayuwarsu ta jihadi.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kara da cewa; Da akwai kyakkyawar rayuwa a gaban al’ummar Yemen, masu dadadden tarihi da kuma ruhin jihadi. Har ila yau, jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; Da akwai bukatar a bude tattaunawa a tsakanin al’ummar Yemen domin kare dukkanin bangarorin addini da kungiyoyin da ake da su a cikin kasar.

 

3834734

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: