IQNA

23:39 - August 16, 2019
Lambar Labari: 3483953
Bangaren siyasa, Hojjatol Islam walmuslimin Kazem Siddighi wanda ya jagoranci sallar Jumaa a Tehran ya bayyana kakkabo jirgin da cewa alama c ta karfin Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran, ya yi kira ga kasar India da ta sauya matakin da ta dauka akan yankin Kashmir

Limamin na Tehran Hojjatol Islam walmuslimin Kazem Siddighi  ya ce: Batun Kashmir matsala ce babba kamar yadda al’ummar musulmin duniya suke kallonta. Ba a kuma tsammaci cewa India za ta dauki matakan da suke cin karo da dokokin kasa da kasa ba. Abin da yake faruwa yana cin karo da hakkokin bil’adama.

Limamin na masallacin juma’ar Tehran ya kuma bukaci ganin gwamnatin ta kasar India ta daina amfani da karfi akan al’ummar musulmin yankin na Kashmir, domin yin hakan yana da sakamako maihatsari.

Limamin na Tehran ya kuma yi suka akan yadda aka yi mu’amala da shugaban Harkar Musulunci ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky a asibitin da aka kwantar da India, da hakan ya yi sanadin komawarsa gida Najeriya.

Dangane da kasar Yemen kuwa, Limamin na Tehran ya kuma yi Magana akan yanayin da kasar Yemen take ciki, yana tabbatar da cewa; A karshe al’ummar kasar ta Yemen ne za su sami nasara.

 

3835234

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، nasara ، kakkabo ، Iran ، Tehran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: