IQNA

23:59 - August 20, 2019
Lambar Labari: 3483971
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan hubbaren Annabi Yusuf (AS) da ke kusa da garin Nablus.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya mutsin ya barke a lokacin da Palasdinawa suke kokarin shiga Hubbaren Anabi Yusuf daidai lokacin da wasu daruruwan yahudawa suke kokarin kutsa kai a harabar hubbaren Annabi Yusu dake gabashin garin Nablus.

Sojojin Isra’ila sun yi amfani da harsashin roba da hayaki mai sa kwalla da kuma bomb mai karan gaske domin tarwatsa palasdinawan.

Shi dai Hubbarren Joseph yana gabar yammacin kogin Jodan ne,yankin da ke karkashin iko gwamnatin kwarya kwaryan cin gashin kai ta palasdinu, don haka sojojin Israila sukan bar mazauna yankin yin ziyara zuwa wajen ba tare da sai sun nemi izini ba, amma sabuwar gwamnatin Natanyaho ta hana musulmi zuwa wajen,

palasdinawa na zargin Isra’ila da shirya makarkashiyar kwace ikon kula da dukkan wuraren tarihi dake yankin,

ko a baya bayn nan na sojojin na Isra’ila sun yi awon gaba da wasu palasdinawa 14 a yammacin kogin jodan da birnin Qudus ba gaira ba dalali.

 

3836374

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: