IQNA

23:48 - September 06, 2019
Lambar Labari: 3484023
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gina masallacia  arewacin birnin Lanadan na kasar Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, masallacin yankin Kentish Town a rewacin birnin Lanadan na shirin kara fadada masallacin domin amfanin musulmin yankin.

Kamal Hussain daya daga cikin masu kula da masallacin yankin ya sheda cewa, a halin yanzu suna yin amfani da wani wuri ne wanda suka jima sukan yin amfani da shi, amma saboda karuwar musulmin yankin, suna bukatar babban wuri.

Ya kara cewa daga shekara ta 2015 suka fara tattara taimako da nufin fadada annan masallaci da suke yin afani da shi, yanzu kuma sun sayi wasu wurare da ke makwataka da wurin, da nufin hade su da masallacin domin kara girmansa.

A halin yanzu akwai fan dubu 800 da aka tara domin wanann aiki, amma ana bukatar fan miliyan daya da dubu dari biyu ne domin aikin.

Masallacin Bait Aman an gina shi a 1998 a arewacin birnin Landan, inda musulmi suke yin amfani da shi, kuma ana sa ran za a kammala aikin fafa shi a cikin 2021.

3840359

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musulmi ، amfani ، Birtaniya ، Landan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: