IQNA

23:35 - September 15, 2019
Lambar Labari: 3484052
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron shekara-shekara na kasa da kasa kan tajwidin kur’ani a Morocco.

Kamfanin dillanin labaran iqna ya habarta cewa, Hassan Alkhabbaz shugaban kwamitin da ke daukar nauyin shirywa wannan taro ya bayyana cewa, za a gudana da aron na bana ne a birnin Kazablanka.

Ya ce wannan shine karo na bakwai da aka shirya wannan taro wanda yake samun halartar malamai da masana da makaranta kur’ani daga sassa na duniya, inda suke gabatar da kasidu da kuma laccoci.

A shekarar da ta gabata na samu halarlar malamai daga kasashe da kuma fitattun makaranta kur’ani na duniya, da suka hada da sheikh Said Muslim, Sheikh Muhammad Alkintawi, Abdulmajid Alsawiri, da kuma Yasin Shehab.

3842191

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: