IQNA

20:13 - September 19, 2019
Lambar Labari: 3484064
Bangaren siyasa, Iran ta gargadi gwamnatin Amurka kan zarginta da kai harin kamfanin Aramco na Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aike da rubutaccen sako zuwa ga ofishin jakadancin Switzerland da ke wakiltar Amurka a Tehran, inda take kalubalatar Amurka kan zargin da ta yi na dora alhakin harin harin Aramco a kan Iran.

A cikin bayanin da ta fitar, ama’aikatar harkokin wajen ta Iran ta bayyana cewa, a jiya ta aike wa gwamnatin Amurka da sako ta hanyar ofishin jakadancin Switzerland, da ke dauke da gargadi kan zargin da Amurka ta yi, na cewa Iran ce ke da alhakin harin ramuwar gayya da dakarun Yemen suka kai kan kamfanin mai na Aramco a Saudiyya.

Bayanin ya ce wannan zargi na Amurka bai ginu a kan wani dalili na ba, jakan kokarin kaucewa kunyar da Amurka ta sha ne, bayan da makaman da ta sayar wa Saudiyya na daruruwan biliyoyin daloli suka kasa kare kasar ta Saudiyya daga hare-haren dakarun Yemen da suke rainawa.

Haka nan bayanin ya yi ishara da cewa, idan Amurka da kawayenta suna son su daina kwasar kunya a idunun mutanen da suke rainawa, to dole ne su kawo karshen kisan kiyashin da suke wa mata da kananan yara a Yemen.

3843091

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kisan kiyashin ، yemen ، Iran ، gargadi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: