IQNA

Harin Taliban Ya Kawo Cikas Ga Zaben Afghanistan

23:53 - September 28, 2019
Lambar Labari: 3484097
Bangaren kasa da kasa, an kai jerin hare hare a lokacin gudanar da zabe a kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, hare haren na daga cikin alwashin da kungiyar Taliban ta tauka na hana gudanar da zabukan data kaurace ma.

Bayanai daga kasar sun ce an kai hare hare a birane da dama na kasar, saidai babu cikaken alkalumma akan irin barna ko hasara da aka samu.

Tunda farko dai an jibge kimanin jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji kimanin dubu dari domin tabbatar da tsaro a zaben wanda ‘yan takara 16 ke fafatawa, ciki har da shugaban kasar mai barin gado.

Kimanin mutane miliyan goma ne sukayi rijisrta a zaben a hukumance, saidai saboda fargaba akan matsalar ta’addanci, ba’a samu fitowar jama’a sosai ba wajen kada kuri’a.

Wasu rahotanni sun ce mutane kadan-kadan ne suka fita zuwa kada kuri’a, a yayin da motocin ‘yan sanda ke sintiri a manyan tituna, musamman a Kabul babban birnin kasar.

3845351

 

 

 

 

captcha