IQNA

23:50 - September 30, 2019
Lambar Labari: 3484104
An samu tashin gobara a tashar jiragen kasa na birnin Jeddah dake kasar Saudiya

Kamfanin dillancin labaran iqna, majiyoyin labaran kasar Saudiya sun sanar da tashin gobara a tashar jiragen birnin jeddah, tare da bayyana cewa har yanzu ba a kai ga gane musabbabin tashin gobarar ba.

Jaridar Sabak ta kasar Saudiya ta ce an dakatar da duk wani kai kawo na jiragen kasa a wannan tasha, tare kuma da kwashe dukkanin fasinjoji da ma'aikatar tashar ganin yadda gobarar ke kara ruruwa.

A nata bangare tashar talabijin din Al-arabiya ta sanar da cewa babu wani mutun da ya rasa ransa ko kuma ya jikkata sanadiyar tashin gobarar.

 

3845829

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Saudiyya ، Jiddah ، gobara
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: