IQNA

23:51 - October 07, 2019
Lambar Labari: 3484127
Bangaren kasa da kasa, kotun Zamfara ta sanar da cewa za a kori duk wani alkali da bai dauki mataki kan keta alfarmar kur'ani ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jaridar Punch NG ta bayar da rahoton cewa, Dahiru Gusau babban alkalin kotun koli ta jihar Zamfara ya bayyana cewa, duk alkalain da aka samu da yin saku-saku wajen daukar mataki kan keta alfarmar kur'ani a jihar, to zai rasa aikinsa.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne aka gano wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka yaga kuma aka saki a ckin shadda a jihar ta Zamfara, lamarin day a daga hankulan al’ummar jihar da ma dukkanin musulmi.

Wannan lamari ya sanya gwamnan Jihar ya bayar da umarnin a gudanar da binciken gaggawa domin gano wadanda suke a hannu wajen keta alfarmar kur’ani tare da hukunta su.

 

 

3847733

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، hukunta ، Zamfara ، Najeriya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: