IQNA

22:51 - October 10, 2019
Lambar Labari: 3484141
Bangaren kasa da kasa, rahotanni na cewa wasu dubban matan ‘yan ta’addan Daesh sun tsre daga arewacin Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, rahotanni sun bayyana cewa ana cigaba da nuna fargaba game da yiyuwar tserewar dubban yan ta’adda dake tsare da gidan yari a kasar Syria bayan da wasu bayanai suke nuna cewa masu tsaron gidajen yarin sun bar wurare.

Bayan kuma suna hadewa da dakarun kudarawa domin tunkarar mataken sojin da kasar Turkiya ta dauka na kai hare- hare kan mayakan kurdawa dake Arewacin kasar Syria.

Ya ci gaba da cewa ana cigaba da tsare daruruwan yan ta’ada na kungiyarda’ashe masu ikirarin jihadi a gidan yarin dake kusa da iyakar kasar Turkiya da Syria.

A wani bayani da shugaban kasar Amurka ya yi, ya nuna cewa akwai fursunonin yan Da’ash masu hadarin gaske da ake tsare da su a gidajen kurku a yankin sai dai tuni aka dauke su zuwa wani wuri mafi tsaro.

 

3848963

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Daesh ، arewacin ، Syria ، Kurdawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: