IQNA

23:06 - October 15, 2019
Lambar Labari: 3484155
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa Iran ta yi amfani da hikima wajen karya kaidin makiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rauhani ya bayyana cewa kawo karshen yakin da Saudiya take jagoranta a kasar Yemen zai iya zama mabudin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Litinin a lokacin da yake amsa tambayoyin yan jarida a Tehran.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa akwai wata tawaga ta kasar hadaddiyar daular larabawa ko hadaddiyar daulolin larabawa da ta zo Tehran domin neman tattaunwa kan rikicin kasar ta Yemen da kuma takaddamar da ke faruwa tsakaninta da wasu kasashen larabawa.

A wani bangaren jawabinsa shugaban ya bayyana cewa Tehran zata ci gaba da shirinta na jingine yarjejeniyar Nukiliya ta shekara ta 2015 matukar kasashen turan da abin ya shafa suka kasa cika nasu alkawullan da suka dauka a cikin yarjejeniyar.

Haka nan kuma ya jaddada cewa kofarkasarsa  bude take ga dukkanin kasashen yankin domin shiga tattaunawa da nufin samun zaman lafiya mai dorewa da fahimtar juna tsakaninsu.

 

3849904

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: