IQNA

Manzon MDD Ya Jaddada Wajabcin Kare Alfarmar Masallacin Aqsa

14:46 - October 31, 2019
Lambar Labari: 3484208
Bangaren kasa da kasa, manzon musamman na majalisar dinkin duniya a Falastinu ya ce dole ne a mutunta masallacin Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wafa cewa, Nicolais Meladunov manzon musamman na majalisar dinkin duniya a Falastinu ya ce dole ne a mutunta masallacin Aqsa tare da kare alfarmarsa.

Ya ce wannan masallaci wuri wanda yake da matukar muhimamnci da kuma yake da matsayi na musamman, wanda kiyaye shi da kuma nisatar aikata duk abin da zai keta alfarmarsa ya zama wajibi.

Manzon musamman na majalisar dinkin duniya a Falastinu ya bayyana hakan ne a lokacin day a kai ziyara  amasallacin, tare da ganawa da babban limami da kuma jami’an falastinawa masu kula da shi, wannan ziyara tana zuwa a daidai lokacin da yahudawa suke ta kara kaimi wajen kutsa kai cikin masallacin tare da keta alfarmarsa.

3853384

 

captcha