IQNA

23:54 - November 01, 2019
Lambar Labari: 3484212
Yahya Nuruddin Abu Taha mahardacin kur’ani ne mai shekaru 7 da haihuwa a Falastinu.

Kamfanin dillancin labaran ya habarta cewa,a  zantawarsa da tashar arabi 21 Yahya Nuruddin Abu Taha ya bayyana cewa, ya samu damar hardace kur’ani ne tae da taimakon mahaifinsa.

Ya cea  halin yanzu yana karatu a firamare, kuma yana fatan zai zama likta a rayuwarsa domin taimaka ma jama’a marassa lafiya, musamman ma marassa karfi daga cikinsu.

Ya kara da cewa, baya ga haka kuma yana da wani babban buri, shi ne yin salla a cikin masallacin Quds, kuma ya cimma wannan buri, domin kuwa a wannan mako ya samu yin salla a cikin wannan masallaci mai alfarma.

 

3853725

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: