IQNA

20:52 - November 19, 2019
Lambar Labari: 3484255
Musulmi a kasar Malawi sun nuna rashin amincewa da matakin hana saka lullubi a wata makaranta a kasar Malawi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kawancen kungiyoyin musulmi a Malawi MAM ya nuna rashin amincewa da matakin hana saka lullubi a wata makaranta a kasar.

Makarantar Agalican ta sanar da cewa dalibai masu saka hijabi a makaranta su daina.

Wannan mataki bai tsaya nan ba, domin kuwa makaranta ta kafa dokar hana daukar duk wata daiba da ta saka lullubi a kanta a wannan makaranta.

Sheikh Dinala Chubulika kakakin MAM ya bayyana cewa, ba za su amince da aka ba, kuma suna kira ga gwamnatin kasar da ta gaggauta daukar matakin taka wa wanann makaranta burki kan hakan.

Duk da umarnin da gwamnati ta bayar na hana korarar dalibai mata masu sanye da lullubi, wannan makaranta tana ci gaba da yin biris da umarnin gwamnatin kasar ta Malawi.

 

3858159

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sanye ، lullubi ، makaranta ، Malawi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: