IQNA

17:27 - December 09, 2019
Lambar Labari: 3484307
Bangaren kasa da kasa, an bude gasar kur’ani ai tsarki ta kasa da kasa a masallacin Zaitunah a kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na Almihwar ya bayar da rahoton cewa, an bude wannan gasa mai take (Imam Hassan Bin Khalaf bin Balimah Alqirawani) ne tare da halartar mahardata da makaranta daga kasashe 21 na duniya.

A yayin bude gasa Ahma Azum ministan ma’ikatar kula da harokin addini, da sheikh Usman Battikh babban mai fatawa na kasar da ma wasu jami’ai da kuma malamai duk sun halarci wurin.

Wanann gasa ana gudanar da ita ne a bangaren harda tafsir da kuma tajwid, kuma tana gudana ne a halin yanzu a babban masallacin Zaituna da ke cikin kasar ta Tunisia.

A ranar farko masu gasa 6 ne suka kara, Amjad Hilal Muhammad Albu Sa’id daga Oman, Haisam Nurul Yakin Bilmahdi daga Aljeriya, Muhammad Amir Alturaiki daga Tunisia, Usama Saleh Muhammad ali daga Jordan, Umar Hamid Abubakar Muhammad Janahi daga Bahrain, Abdulkadir Mu’ammar Miftah Kindi.

Abu Ali Alhassan Bin Khalaf Bin Abdullah Bin Billaimah Aharazi Alqirawani, ya kasance daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani na kasar, wanda aka haife shi a cikin shekara ta 427 ko 428 hijira kamariyya a kasar ta Tunisia.

 

3862488

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: