IQNA

19:13 - December 15, 2019
Lambar Labari: 3484321
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taro kan musulunci na daliban jami’oi a kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ana shirin gudanar da zaman taro kan musulunci na daliban jami’oi a kasar Ghana a daidai lokacin da za a gudanar da irin wannan taroa  biranaen Kano da Lagos da ke Najeriya.

Babbar manufar taron dai ita ce kara wayar da kan daliban jami’oi na kasashen Afrika kan hakikanin koyarwar addinin mulunci, da sahihin tarihin muslunci, da yadda ya kamata musulmi su himmatu wajen samar da ci gaban kasashensu da al’ummominsu.

Daliban jami’oi daga kasashen najeriya, Ghana, saliyo, Ugaganda, Liberi, Gambia da dai sauransu ne za su halarci zaman taron wanda zai gudana a kasahen na  Ghana da kuma Najeriya a cikin mako mai zuwa.

A baya an gudanar da irin wannan taro a birnin Accra na kasar Ghana, wanda ya samu halartar daruruwan dalibai daga kasashen Afrika da dama.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3863943

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Ghana ، Najeriya ، Saliyo
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: