IQNA

22:29 - December 19, 2019
Lambar Labari: 3484333
shugaban kasar Labanon, Michel Aoun, ya nada Hassan Diab, a matsayin sabon firaministan kasar, wanda zai kafa sabuwar gwamnati.

Mista Diab, zai maye gurbin Saad Hariri, wanda ya yi murabus daga mukamin sakamakon zanga zangar data mamaye kasar.

Sabon firaminsitan Hassan Diab, na samun goyan bayan kungiyar Hezbollah ta kasar.

Shi dai Hassan ba sananne sosai ba a idon al’ummar kasar, amma ya taba rike mukamin ministan ilimi a shekara 2011.

Tun a cikin watan Oktoba ne kasar ta Labanon ke fama da jerin zanga zanga na al’ummar kasar dake kin jinin mahukuntan kasar da suke zargi da cin hanci da rashawa.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3865314

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، zanga-zanga ، lebanon
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: