IQNA

Zaman Tattaunawar Hadin Kan Musulmi A Afrika Ta Kudu

13:21 - December 23, 2019
Lambar Labari: 3484339
An gudanar da wani zaman tattaunawa na hadin kai tsakanin musulmi a kasar Afrika ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a jiya gudanar da wani zaman tattaunawa na hadin kai tsakanin musulmi a birnin Pretoria, tare da halartar Ahmad Ali Mohsenzadeh, da kuma shugaban cibiyar musulunci Farhad Hussain, gami da wasu masana musulmi.

Yusuf Mustafa shugaban tashar talabjin ta musulmin kasa Afrika ta kudu ya bayyana cewa, babban abin da ke da muhimmanci sakanin musulmi a halin yanu shi ne hadin kai. Ya ce marigayi Imam Khomeni (R) ya jaddada wajabcin wannan hadin kai a shar’ance.

Abdulaziz Sheikh daya daga cikin mambobin cibiyar musulmin Afrika ta kudu ya gabatar da nasa jawabin a wurin wannan taro, inda shi ma ya jaddada matsayarsu ta neman hadin kan musulmi.

Ahmad Matir wani fitaccen marubuci ne dan kasar Afrika ta kudu uma musulmi, wanda shi ma ya halarci wurin taron ya gabatar da nasa jawabin a kan wannan maudui da muhimmancinsa.

Rubina Qur wata fitacciyar yar jarida ce a kasar, wadda ta samu halartar wurin taron, kuma ta gabatar da jawabi kan muhimmancin hadin kan musulmi, da yadda hakan zai iya ba su karfi a siyasance a duniya.

Dukkanin wadanda sukahalarci taron da suka hada da malamai da masana ‘yan shi’a da ‘yan sunnah, sun gabatar da mahanga iri guda wadda ta ginu a kan wajabcin hadin kai na girmama juna, inda daga karshe Sheikh Mustaf daga cikin malaman jami’ar Al-mustafa (SAW) ya gabatar rufe da bayanin karshe.

https://iqna.ir/fa/news/3865700

captcha