IQNA

0:54 - December 25, 2019
Lambar Labari: 3484342
Dubban musulmin kasar Ethiopia sun yi xamga-zangar nuna adawa da kona masalatai da wasu ke yi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a yau dubban musulmin kasar Ethiopia sun yi xamga-zangar nuna adawa da kona masalatai da wasu ke yi a wasu yankunan kasar.

Wannan mataki an zuwa bayan da wasu matsanin kiyayya da addinin muslunci suka fara kai hare-hare a kan wasu masallatai na musulmi  akasar.

An kai hare-haren ne a garin amhara, wanda akasarin mazaunansa kabilu ne mabiya addinin kirista, duk kuwa da cewa kafin wannan lokaci babu wata matsala tsakaninsu.

Dangane da wannan batu firayi ministan kasar yay i tir da wanann mataki, inda ya bayyana cewa wasu ne suke son mayar da hannun agogo baya  akasar.

Kiamnin kashi biyu bisa uku na mutanen kasar Ethiopia dai mabiya addinin muslunci ne, yayin da sauran kuma mabiya addinin kirista ne, sai kuam yan kadan masu da’awar bin addinin yahudanci.

 

https://iqna.ir/fa/news/3866185

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: