IQNA

15:27 - January 04, 2020
1
Lambar Labari: 3484375
Babban sakataren Hizbullah ya fitar da bayani kan kisan da Amurka ta yi wa Qasem Solaimani da kuma mika sakon ta’aziyya ga Imam Khamenei.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren Hizbullah ya fitar da bayani dangane da kisan da Amurka ta yi wa Qasem Solaimani da kuma Abu Mahdi Almuhanddis, tare da bayyana shahadarsu a matsayin babban lamari, a kan tafarkin Imam Hussain (AS) da Sayyida Zainab (AS).

Ya ce ko shakka babu Amurka ta tafka babban kure ta hanyar tafka wannan laifi na ta’addanci da ta yi, kuma ta sani cewa mayar da martani kan wannan ta’addanci aikin ‘yan gwagwarmaya ne, saboda haka sai Amurka ta zama cikin shiri.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa; Amurka ba za ta cimma ko daya daga cikin manufofinta ba ta hanyar kisan wadannan bayanin Allah, a daidai lokacin da Qasem Sulaimani manufofinsa za su ci gaa da tabbata, domin akwai miliyoyi da suke a kan tafarkinsa, kuma kisansa ya kara musu karfin gwiwa.

Daga karshe ya mika sakon ta’aziyya ga al’ummomin Iran da Iraki dangane da wanann shahada ta wadannan manyan kwamandojin gwagwarmayar yaki da zalunci da babakere na manyan masharranta na duniya ‘yan mulkin mallaka a kan kasashen musulmi da kasashe ranana.

 

https://iqna.ir/fa/news/3868552

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
1
soko daga ni aminullah al gulami allah yasa jinin shahid qaseem sulaiman ya jawo sanadin hallaka amurka da sahayuniya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: