IQNA

16:13 - January 07, 2020
Lambar Labari: 3484388
Firayi ministan kasar Malaysia ya bayyana cewa, kisan Qassem Sulaimani ya sabawa dokokin duniya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Mahatir Muhammad ya gargadi gwamnatin kasar Amurka da cewa, kisan Qassem Sulaimani zai iya jawo manyan matsaloli a yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce wanann aikin daidai yake da kisan da aka yi wa Jamal Khashoggi dan jaridar kasar Saudiyya a cikin kasar Turkiya, wanda ya shiga Turkiya tare da izini, wanda kisansa babban laifi ne na kasa da kasa.

Da jijjifin safiyar Juma’a da ta gabata ce dai Amurka ta kaiwa Janar Qassem Sulaimani hari tare da Abu Mahdi Almuhanddis a kusa da filin jirgin sama na Baghdad, inda suka yi shahada tare da mutane da ke tare da su.

 

https://iqna.ir/fa/news/3869907

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: