IQNA

12:11 - January 09, 2020
1
Lambar Labari: 3484397
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, jinin Sulaimani ne zai tilasta wa Amurkawa ficewa daga yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a birnin Tehran, ministan harkokin wajen Iran Muhammad jawad Zarif ya bayyana cewa, Amurkawa da kansu ne suka bude kofar ficewarsu daga yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce kisan da suka yi wa Kasim Sulaimani shi ne babban abin da zai tilasta su ficewa daga yankin, juma kowa ya fara ganin sakamakon hakan.

Zarif ya ci gaba da cewa, martanin da Iran ta mayar wanann wani abu ne na daban, ba zai taba zama daidai da aikin ta’addanci na kisan Kasim sulaimani ba, wanda kuma Amurka ta fahimci hakan sakamakon babban kuren da ta tafka.

Dangane da batun mayar da martani kan Amurka a cikin kasar Iraki kuwa, Zarif ya bayyana cewa, tun kafin kai harin Iran ta sanar da mahukuntan kasar Iraki cewa za ta mayar da martani kan sansanin sojin Amurka.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870245

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، muhammad jawad zarif ، Iran ، Amurka ، sansanin sojin Amurka
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Kadan sukagani.
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: