IQNA

21:47 - January 09, 2020
Lambar Labari: 3484399
Ilhan Omar ‘yar majalisar dokokin kasa Amurka ce wadda take adawa da siyasar Trump ta yaki a kan Iran.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Ilhan Omar ‘yar majalisar dokokin kasa Amurka musulma ta yi Allawadai da yunkurin kara takunkumi a kan Iran.

Ita dai ‘yar asalin kasar Somalia ce, wadda ta yi hijira zuwa Amurka shekaru 20 da suka gabata, inda ta bayyana a shafinta na twitter cewa, ni na fito daga yankin da yaki ya daidaita, saboda haka Trump ka sani cewa ba sai ta hanyar yaki ne kawa za ka iya yin kasuwanci ba da cin riba ba.

Ta kara da cewa tana kira ga jama’a da su fito su yi zanga-zanga domin nuan kiyayya ga salon siyasar ina da yaki ta Donald, wanda ke neman jefa Amurka cikin wani sabon bala’i.

Ta ce hankoron kara saka wa Iran takunkumi a tunani ne na hankali ba, domin kuwa takunkuman da aka saka wa kasar in banda cutar da al’umma marassa karfi babu abin da ya haifar.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870446

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: