IQNA

23:25 - January 22, 2020
1
Lambar Labari: 3484440
Majalisar dattijan murka tana ci gaba da sauraren bayanai kan batun bukatar neman a tsige Trump daga kan mulki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a yammacin jiya Talata ne dai majalisar dattijan Amurka za ta fara sauararen bayanai kan batun neman tsige Donald Trump daga kan kujerar shugabancin kasar.

A yau majalisar dattijan kasar ta Amurka ta sanar da cewa tana ci gaba da sauraren bayanai kan zarge-zargen da ake yi wa Donald Trump, wanda ka iya kaiwa ga tsige daga kan kujerar shugabancin kasar ta Amurka.

Amma a nasu bangaren lauyoyi masu kare Trump sun bukaci majalisar dattijan da ta yi watsi da wannan batun, domin kuwa a cewarsu wanann ya sabawa doka, kuma yin hawan kawara ga lamarin dimukradiyya a kasar ta Amurka..

A ranar sha daya ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce dai majalisar wakilai ta fara sauraren bayanai na shedu kan zarge-zargen da ake yi kan Trump.

Ana zarginsa da laifuka da suka hada da yin amfani da kujeararsa domin buri na siyasa don kashin kansa, inda ya tilasta shugaban Ukraine da ya bayar da wasu bayanai kan dan takarar shugabancin kasar Amurka karkashin inuwar jam’iyyar Democrat Joe Baiden, wanda hakan ka iya kayar da shi, domin shi Trump din ya samu nasara a zabukan shugaban kasa.

Sannan kuma baya ga haka kuma akwai batun cewa yana yin gaban kansa a cikin lamurra, ba tare da girmama majalisa ba, ta hanyar kin bayar da hadin kai ga majalisar wajen gudanar da bincike kan batun.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3873367

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Yahaya abubakar bagaya
0
0
Atsige shi bamakawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: