IQNA

22:46 - January 25, 2020
Lambar Labari: 3484448
Wasu ‘yan wasa mata musulmi a kasar Amurka sun bayyana yadda ake nuna musu banbanci saboda tufafinsu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin Toledo Blade cewa, a wani taro da aka gudanara  jami’ar (Lourdes University) da ke Amurka, ‘yan wasan uku sun bayyana yadda ake nuna musu wariya saboda shigar musulunci da suke yi.

Wata kungiya mai suna let Noor Run ce ta shirya zaman taron, inda Balkis Abdulkadir ‘yar wasan kwallon Kwando, da Amaya Zafar ‘yar wasan dambe, da kuma Nur Alexendria Abu Karam suka halrci wurin.

Dukkaninsu sun bayyana yadda suke fuskantar matsaloli a wurin wasa, kama daga wurin hukumoin da suke jagorantar harkokin wasannin, da kuma wurin ‘yan kallo da suke yi musu izgili, saboda suna sanye da lullubi a  kansu.

Abu karam ta ce irin wannan yanayi yana yin mummunan tasiri a cikin zuciyar dan wasa, domin kuwa yana yin iyakacin kokarinsa amma baya samun abin da zai karfafa gwiwarsa daga bangaren jami’ai da kuma ‘yan kallo, saboda ya rike wani abu da yashfi addininsa, wanda kuma ba zai hana shi aiwatar da wasan yadda ya kamata ba.

 

https://iqna.ir/fa/news/3873923

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: