IQNA

22:59 - January 27, 2020
Lambar Labari: 3484453
Kungiyoyin falastinaw sun yi watsi da shirin Amurka da da ake kira da yarjejeniyar karni ko mu’amalar karni.

Shafin yada labarai na Alahad ya bayar da rahoton cewa, Khalid Batash daya daga cikin jagororin kungiyar jihadul Islami ya bayyana cewa, dukkanin falastinawa da ke cikin yankunan da Isra’ila ta mamaye a 1948, ba su amince da yarjejeniyar karni ba.

Ya ce wannan ba wani abu ba ne face sabuwar yaudara da nufin sayar da batun falastinu, da mika al’ummar falastinu kyauta ga Isra’ila.

Shi ma a nasa bangaren Fauzi Barhum, kakain kungiyar Hamas ya bayyana cewa, wannan yunkuri na Amurka da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa, babbar cin amana ce ga al’ummar falastinu.

Ya ce; da a ce wasu daga cikin kasashen larabawa ba su zama ‘yan kanzagi da amshin shata ga Amurka ba, to da Amurka da Isra’ila ba su samu damar kirkiro wani shirin mamaye falastinu a hukumance ba.

Nabil Abu Rudaina shi ne kakakin kwarya-kwaryar gwamnatin cin gishin kai ta falastinawa, ya bayyana cewa; ko da wasa al’ummar falastinu ba za su taba mika wuya ga wannan sabuwar yaudara da Trump da ‘yan korensa suka kirkiro ba.

Dukkanin sauran kungiyoyin falastinawa da jam’iyyun siyasa da kuma kungiyoyin masu fafutuka duk sun fitar da bayanai daya bayan daya, da ke yin tir da wannan shiri na mu’amalar karni, tare da shan alwashin cewa ba zasu taba amincewa da ita ba.

Wannan shiri dai Amurka da Isra’ial suka kirkiro shi, wanda yake samun goyon bayan gwamnatocin Saudiyya da Masar gami da Jordan.

 

https://iqna.ir/fa/news/3874196

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: