IQNA

Saudiyya Ta Ce Lokaci Bai Yi Ba Na Karbar yahudawan Isra’ila A Yanzu

19:41 - January 28, 2020
Lambar Labari: 3484457
Bangaren kasa da kasa, Saudiyya ta bayyana cewa lokaci bai yi ban a karbar yahudawan Isra’ila a cikin kasarta.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa basu shirya karbar ziyarar ‘yan Isra’ila ba, kwana guda bayan da Isra’ilar ta bayyana cewa ta bai wa ‘yan kasarta ‘yancin ziyartar Saudiyya domin gudanar da ayyukan ibada da kuma harkokin kasuwanci.

Da yake bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na CNN, ministan harkokin wajen Saudiyya, Faisal ben Farhane al-Saoud, ya jaddada cewa kasarsa ba ta da hulda da Isra’aila, a don haka masu dauke da fasfon Isra’ila ba zasu iya kai ziyara Saudiyya ba a daidai wannan lokaci .

A ranar Lahadin da ta gabata ce a karon farko ministan cikin gidan Isra’ila, Aryeh Deri ya sanya hannu domin amince wa yahudawa yin balaguro kai tsaye zuwa Saudiyya, domin gudanar da ayyukan ibada da kuma harkokin kasuwanci, a wani mataki da ake kallo a matsayin karfafa dangantaka tsakanin Isra’ila da Saudiyyar.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3874706

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha