IQNA

23:04 - January 30, 2020
Lambar Labari: 3484465
Dubban a'ummar kasashen Bahrain da Jordan ne suka fito kan tituna domin yin tir da abin da ake kira yarjejeniyar karni da Trump ya gabatar kan palestine.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, dubban mutane ne suka fito a kan manyan tituna a dukkanin biranan Jordan domin nuna rashin amincewarsu da shirin na Amurka da ake kira yarjejeniyar karni.

Masu jerin gwanon sun yi ta rera taken mutuwa ga Amurka mutuwa ga Isra’ila, yarjejeniyar karni yaudara ce da munafunci, haka nan kuma sun yi ta rera taken yin kira ga gwamnatin Jordan da ta kori jakadan Isra’ila da ke a kasar.

Tashar Almanar ma ta bayar da rahoton cewa a kasar  Bahrain ma mutane sun gudanar da irin wanann jerin gwanon, inda suke bayyana wannan shiri da cewa yunkuri ne na sayar da falastinu.

Haka nan kuma masu gangamin sun rika rera taken cewa Amurka ce ne babbar shaidan na duniya.

 

https://iqna.ir/fa/news/3875281

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Bahrain ، Trump ، hotuna
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: