IQNA

Za A Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Domin Yaki Akidar Kyamar Musulmi

23:53 - February 03, 2020
Lambar Labari: 3484480
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudana da zaman taron yaki da akidar kyamar musulmi a jihar Minnesota ta kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na ODT ya bayar da rahoton cewa, cibiyar musulmin kasar Amurka CAIR za ta dauki nauyin shirya wani taro na kasa da kasa, wanda zai yi dubi a kan kyamar musulmi da kuma hanyoyin dakile wannan akida a Amurka da ma duniya.

Jamal Foda limamin masallacin Al-nur a kasar Newzealnd wanda aka kaiwa hari a shekarar da ta gabata, yana daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a wurin taron.

Foda ya jagoranci wani taro bayan kai harin masallacin Nur a birnin Christchurch na kasar Newzealand, inda dubban mutane suka samu halarta, da hakan ya hada har da firayi minista ta kasar, inda ya bayyana cewa musulmi ba za su biye wa aikin 'yan ta'adda ba, za su yi aiki ne da koyarwar addininsu ta zaman lafiya da girmama juna tsakaninsu da sauran al'ummomi.

Taron na yaki da kyamar musulmia a Amurka zai guna nea  ranar 17 ga watan maris mai zuwa a jihar Minnesota ta kasar Amurka.

A can birnin Christchurch an kasar Newzealand ma ofishin magajin garin birnin ya shirya zaman taro a ranar 15 ga watan Maris domin girmama musulmin da suka rasa rayukansu sakamakon harin ta'addanci a  cikin masallaci.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876095

captcha