IQNA

23:42 - February 05, 2020
Lambar Labari: 3484487
Bnagaren kasa da kasa, Ministan harkokin wajen Iran Jawad Zarif ya zanta da shugaban falastinawa ta wayar tarho.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da goyan bayan kafa gwamnatin Palasdinu da ta kunshi Qudus babban birni.

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas Abu Mazin.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya kuma kalubalanci yarjejeniyar da ake dangantawa data karni ta shugaba Donald Trump na Amurka kan rikicin Palasdinawa da yahudawan mamaya na Isra’ila.

A kan haka a cewarsa Iran, za ta ci gaba da tsayin daka kan al’ummar Palasdinu, na samar wa kansu ‘yanci da kafa gwamnati mai babban birni a Qudus.

Mahukunatan Palasdinawa dai sun yi watsi da tsarin na Trump, wanda suka ce tuni ya shiga kwadon shara na tarihi.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876647

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: