IQNA

23:57 - February 12, 2020
Lambar Labari: 3484516
Al'ummar lardin Karkuk na kasar Iraki sun gudanar da tarukan tunawa da Kasim Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis bayan cikar kwanaki arba'in da shahadarsu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, an gudanar ad wadannan taruka a yankuan daban-daban na lardin Karkuk na kasar Iraki, inda jama'a suka taru aka gabatar da jawabai da kuma daga hotuann wadannan mutane biyu a ko'ina.

Al'ummar lardin Karkuk sun bayyana wadannan mutane biyu a matsayin gwarazansu, kasantuwar cewa Kasim Sukaimani da Abu Mahdi Muhandis su ne suka 'yantar da garuruwansu, bayan da 'yan ta'addan Daesh suka killace garuruwa na tsawon watanni fiye da uku.

Jama'a sun yi Allawadai da kisan wadannan manyan gwaraza biyu da Amurka ta yi, tare da bayyana hakana  matsayina ikin ta'addanci.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878305

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: