IQNA

Jamus: An Killace Masallacin Fateh Bisa Jita-Jitar Dana Bam A Cikinsa

15:34 - February 26, 2020
Lambar Labari: 3484562
Tehran – (IQNA) sakamakon wani bayani da aka samu kan yiwuwar dana bam a masallacin Fateh a kasar Jamus, an killace massalacin.

Jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, bayan samun wani bayani da ke nuni da cewa an dana bam a masallacin Fateh a kudu maso yammacin kasar Jamus, jami’an tsaron sun bukaci mutane su bar wurin, kuma sun killace masallacin.

A daren jiya ne kwamitin masallacin ya samu sako na email, wanda yake cewa an dana bam a cikin wannan babban masallaci, wanda hakan yasa musulmi suka nisanta daga wurin tun daga daren jiya Talata.

Bayan gudanar da bincike ba a samu wata alama ta bam ba, amma duk da haka dai jami’an tsaron kasar ta Jamus sun bukaci musulmi da kaurace wa wurin har zuwa lokacin kammala bincike.

Aana zaton cewa wasu masu tsananin kiyayya da musulmi a kasar ta Jamus ne suka aike da wannan sako, domin saka musulmi cikin zullumi.

3881636

 

captcha